An kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama a wani harin makamai masu linzami a birnin Kyiv a yau Asabar, a cewar Magajin Garin Kyiv Vitali Klitschko.
Klitschko ya ƙara da cewa ma’aikatan lafiya na kula da waɗanda aka raunata.
Ya kuma bayyana cewa, janar-janar na Rasha sun yi barazanar ƙarin wasu hare-haren a kan babban birnin.
A cewarsa, makaman ba da kariya daga sama na yunƙurin kare rayuwar mutane, “amma maƙiyan ba su da imani”.