fidelitybank

Rasha ta kashe mutane 60 a cikin makaranta – Ukraine

Date:

Mutum kusan 60 ake fargabar sun mutu, bayan wani bam ya tashi a wata makaranta a Gabashin Ukraine, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da sojojin Rasha da ƴan aware.

Gwamnan yankin Luhansk, Serhiy Gaidai, ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yana mai cewa, mutum 60 ne ake fargabar sun mutu a ƙarƙashin ɓaraguzan makarantar da ke Bilohorivka.

Ya kara da cewa, kimanin mutane 90 ne ke zaune a cikin ginin kuma an ceto 30, bakwai daga cikinsu sun samu raunuka.

BBC ta rawaito cewa, Mista Gaidai ya ce, wani jirgin Rasha ne ya jefa bam a ranar Asabar.

Ba a iya tantance zargin nasa kai tsaye ba kuma babu wani martani da Rasha ta mayar.

Luhansk ya kasance yanki na fagen yaƙi yayin da sojojin Rasha ƴan aware ke neman yi wa dakarun gwamnatin Ukraine ƙawanya dakarun gwamnati, tsawon watanni biyu da fara mamayar Rasha.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp