An ce sama da mutun 5,000 ne suka yi fito zanga-zanga a Moscow da St Petersburg da sauran biranen Rasha.
Kungiyar da ke sa ido ta OVD ta ce ta tattara alƙalumma a wurare fiye da 50 a cikin Rasha, ciki har da Irkutsk a Siberiya da Vladivostok a gabas mai nisa.
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar suna yayata kalamai na adawa da yaÆ™i kuma suna bayyana cewa ‘Ukraine ba maaÆ™iyarmu ba ce’.
Kungiyar OVD ta ce an tsare masu zanga-zangar adawa da yaƙin Ukraine sama da 12,000 tun lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamayar.