fidelitybank

Rasha ta kama mutane fiye da 600 a kan kyamatar yakar Ukraine – OVD

Date:

Masu zanga-zanga fiye da 600 aka kama a garuruwan Rasha 21, a cewar wata ƙungiya mai lura da lamurra OVD-Info, bayan sun fito nuna ƙin jinin yaƙin da ƙasarsu ta ƙaddamar a Ukraine.

Ƙungiyar ta ambato kafofin yaɗa labarai na Rasha na cewa an tsare mutum fiye da 200 a birnin Novosibirsk da ke yankin Siberia.

Jagoran adawa Alexi Navalny ya yi kiran a fito zanga-zanga a manyan dandali da ke ƙasar da ƙarfe 2:00 agogon ƙasar (12:00 agogon Najeriya) a biranen Moscow da St Petersburg.

An daɗe ana tsare da masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Rasha. OVD-Info ta ce, aƙalla mutum 8,000 aka tsare ko aka kama a Rasha tun bayan ƙaddamar da yaƙi a Ukraine kwana 11 da suka wuce. A rahoton BBC.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp