fidelitybank

Rasha ta kama ƴan agaji biyu na Birtaniya a Ukraine

Date:

Wata kungiyar agaji ta ce, Rasha ta kama wasu ma’aikatan agaji biyu ‘yan Birtaniya.

Kungiyar agajin mai suna, Presidium Network ta ce, an tsare mutanen ne a wani shingen da Rasha ta kafa kusa da birnin Zaporizhzhia a kudancin Ukraine tun ranar Litinin.

Daya daga cikin jagororin kungiyar ta Presidium Dominic Byrne, ya ce ma’aikatan na kokarin ceto wasu ‘yan gida daya ne da yakin ya rutsa da su.

“Sun sami wuce wani wurin bincike da sojojin Ukraine suka kafa a hanyar su ta zuwa kudancin yankin sai dai zuwa ranar Litinin ba mu kara ji daga garesu ba,” kamar yadda ya sanar da wani shirin talabijin na BBC Breakfast.

Ya ce mutanen da ke jiran su ceto su, sun rinka samun sakonni daga wayar ‘yan Birtaniyan biyu, kuma bayan sa’o’i biyu sai sojojin Rasha suka kutsa cikin gidan, sun tambayi alakarsu da ma’aikatan agajin, a matsayin ‘yan leken asiri ne.

Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ta c,e tana kokarin sanin halin da suke ciki.

vanguard newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

IGP ya ba da umarnin bincike kan bidiyon ƙorafin wani tsohon ɗansanda

Babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya...

Amurka za ta bayar da gudunmawar dala miliyan 30 ga ‘yan Gaza

Amurka za ta ba da tallafin dala miliyan talatin...

Iran na binciken ɓarnar da aka yi cibiyoyin nukiliyar ƙasar

Ministan harkokin waje na Iran ya amince an yi...

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karo na farko

Japan ta zartar da hukuncin kisa a karon farko...

Sojoji na zaman makoki na kwanaki 3 bayan an kashe Jami’ai 17

Rundunar Sojin sama ta bayyana fara zaman makoki na...

‘Yan Ta’adda ba za su samu mafaka ba a Nasarawa ba – Gwamna

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya musanta zargin da...

Sojoji sun mayar da martani kan ‘Yan ta’addan Neja

Dakarun Sojin Saman kasar nan, sun ce sun ƙaddamar...

Kotu ta yanke wa Matashin da ya kashe Budurwarsa hukuncin kisa

Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan...

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da...

Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanya hannu kan...

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...
X whatsapp