Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta ƙaddamar da ”munanan hare-haren makamai masu linzami 120 da jirage marasa matuƙa 90 a duka yankunan Ukraine’
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Telegram, shugaban na Ukraine ya ce Rasha ta ƙaddamar da hare-haren ne kan tashar samar da makamashi ta Ukraine.
Mista Zelensky ya ce wasu sassan ƙasarsa a yanzu haka ba su da wutar lantarki, amma ya ce ana koƙarin maido da ita.
Shugaba Zelensky ya ƙara da cewa rundunar tsaron samaniyar kasa ta kakkaɓo fiye da makamai 140.