Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kai hari ta hanyar amfani da makami mai tsananin gudu kan abin da ta kira ma’adanar makamai da ke yammacin Ukraine.
Igor Konashenkov ya yi iƙirarin cewa wurin adana makaman na ƙunshi ne da makamai masu linzame da makaman jiragen sama na sojojin Ukraine.
Rasha ba ta taɓa cewa ta yi amfani da makamin ba mai tsananin gudu a fagen yaƙi.
Makami ne da ke bala’in gudu fiye sau biyar na gudun sauti.