Yakin Rasha a Ukraine ya ja wa Ukraine asarar fiye da dala biliyan 564 ya yanzu.
Yakin ya lalata mata gine-gine masu muhimmanci da kuma durkushewar ci gaban tattalin arzikinta.
Rasha na ci gaba da cewa ta na gudanar da wani babban farmaki a Ukraine da nufin durkusar da sojojin Ukraine. In ji BBC.
Ukraine da kawayenta sun ce, wadannan kalamai na Rasha wani uzuri ne na mamayar da take yi babu gaira ba dalili.