Mutum tara ne suka mutu wasu 57 suka jikkata a wani hari da aka kai yammacin Ukraine, in ji gwamnan yankin Lviv Maksym Kozytsky.
Hukumomi na ta kokarin kashe wutar da ta tashi a sansani, a lokacin da ya gayawa taron manema labarai.
Maksym Kozytsky ya ce, Rasha ta harba makaman roka sama da 30 kan sansanin Yavoriv.
An ta ganin motocin asibiti na kai kawo a yankin zuwa sansanin.