Rasha ta haramta duka wasu jirage da ke da alaƙa da Birtaniya shiga ƙasarta.
Wannan na zuwa ne bayan da Birtaniya ta dakatar da kamfanin jirgin saman Rasha wato Aeroflot daga shiga Birtaniya bayan Rashar ta kai hari ga Ukraine.
Kasar Rasha ta bayyana matakin na ta a matsayin martani kan takunkuman da Birtaniya ta saka mata ta ɓangaren jiragen sama.