Hukumar da ke kula da kafofin yaɗa labarai a Rasha ta hana shiga shafukan wasu kafofin labarai na ƙasashen Yamma, ciki har da BBC bayan masu shigar da ƙara sun yi mata ƙorafi.
Hukumar Roskomnadzor ta ce, sauran shafukan labaran da ta toshe sun ƙunshi Deutsche Welle ta Jamus, da Meduza, da kuma na gidan rediyo mai yaɗa shiri cikin Rashanci wanda Amurka ke kula da shi mai suna Radio Liberty.
Tun a farkon mako ƙungiyar Tarayyar Turai ta toshe wasu kafafen yaɗa labarai na Rasha daga ƙasashe mambobin ƙungiyar, ciki har da gidan talabijin na RT da Sputnik.
Wannan ya biyo bayan rincaɓewar yakin da Rasha ke yi wa Ukraine.