Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya gargadi Koriya ta Kudu cewa, za ta tafka babban kuskure har idan ta sake ta bai wa Ukraine makamai a yaƙin da take yi da Rasha.
Kalaman Putin na zuwa ne bayan da babbar birnin ƙasar Koriya ta Kudu, Seoul ta ce tana la’akari da yiwuwar hakan, a matsayin martani ga sabuwar yarjejeniyar da Rasha da Koriya ta Arewa suka ƙulla na taimakawa juna a yayin da ake kai hari kan ko wace kasa.
Gwamnatin Rasha za ta yanke hukuncin da ba laile su yi wa Koriya ta Kudu daɗi ba idan har ta yanke shawarar samar da makamai ga Ukraine.
Putin ya bayyana hakan ne ga magana ne a kasar Vietnam, jim kaɗan bayan wata gagarumar ziyarar da ya kai birnin Pyongyang ta kasar Koriya ta Arewa, wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da shugaban Koriyar Kim Jong Un.
Putin ya kuma yi gargaɗin cewa Moscow za ta bai wa Pyongyang makamai idan har Amurka da ƙawayenta suka ci gaba da bai wa Ukraine makamai.