Rasha ta umarci wasu jami’an diplomasiyyar Amurka biyu da ke ofishin jakadancin Amurka a ƙasar da su fice daga ƙasar.
Cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ta bai wa Jeffrey Sillin da David Bernstein wa’adin mako ɗaya su fice daga Rasha
Sanarwar ta zargi jami’an biyu da yin wasu abubuwa da suka ‘saɓa ƙai’ida’.
Haka kuma Rasha ta zargi mutanen biyu da yin alaƙa da tsohon ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka a Vladivostok, Robert Shonov, wanda Rasha ta zarga da tattara bayanai kan ayyukan sojinta a Ukraine.
Robert Shonov ya yi aiki da ofishin jakadancin Amurka a Vladivostok na fiye da shekara 25, kafin Rasha ta bayar da umarnin korarsa a shekarar 2021. In ji BBC.


