fidelitybank

Rasha ta ci tarar manhajar Google dala 135,000

Date:

Wata kotu a birnin Moscow ta ci tarar kamfanin Alphabet mamallakin Google saboda ya ki cire wasu bidiyo da suke takaddama a kai tsakaninsu.

An ci tarar katafaren kamfanin fasahar zamanin sau biyu – wadanda jumilla sun kai rouble miliyan 11 ($135,000), saboda ya taka dokar Rasha.

Wata kotu a gundumar Tagansky a Moscow ta cekamfanin ya yada bayanan da ba na gaskiya ba ne kan yawan dakarun Rasha da suka mutu a Ukraine.

Daya daga ckin bidiyon ya nuna wata hira ta wayar tarho tsakanin wasu sojojin Rasha da ‘yan uwansu a gida. Bidiyon ya nuna wai suna kokawa kan yawan wadanda suka mutu ne a cikinsu.

Baya ga Google, Rasha ta toshe wasu fitattun kafofin sadarwa kamar Facebook da Instagram, amma YouTube na nan yana aiki.

Google ya taba fuskantar hukunci a Rasha a shekarun baya. An taba cin sa tarar rouble biliyan 7.2 a watan Disambar 2012 saboda ya ki sauke wasu bayanai da suka taka dokokin kasar Rasha.

latest news in nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp