Ministan harkokin wajen ƙasar Rasha Sergei Lavrov, ya gabatar da wani kakkausan jawabin nuna adawa da ƙasashen Turai, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York.
Mista Lavrov ya zargi Amurka da ƙawayenta da kirkiro abun da ya kira ”Daular karya, da farfaganda”.
Ya ce idan ka kalli yawan kuɗin da Amurka da Nato da ƙasashen Turai suka kashe wajen goyon bayan gwamnatin Kyiv da wani rahoto ya ce yawansu ya kai dala biliyan 170 daga Fabrairun bara zuwa yanzu, za ka gane irin tunaninsu.
Ya kuma yaba da yadda kungiyar BRICS ta ƙasashe masu haɓakar tattalin arziki ke bunƙasa, yana mai cewa a yanzu an samu zaɓi tsakanin karya da gaskiya, dimokraɗiyya da kuma babakere.