Hukumomin kasar Rasha sun tabbatar wa ‘yan Najeriya da ke cikin ƙasar cewa, za a ci gaba da ba su tallafin da suka dace, domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da jin dadinsu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Moscow na kasar Rasha ya fitar ranar Juma’a a gefen taron da jami’an kasashen biyu suka yi.
Ganawar ta kasance tsakanin, Farfesa Abdullahi Shehu, jakadan Najeriya mai cikakken iko a kasar Rasha tare da amincewar kasar Belarus, da Mikhail Bogdanov, wakilin Tarayyar Rasha a Gabas ta Tsakiya da Afirka.
Bogdanov, wanda kuma shi ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, ya ba da tabbacin a ganawar da suka yi da Shehu a ofishinsa.
Sanarwar ta ce: Bogdanov ya sanar da Shehu game da shirye-shiryen dabaru da Rasha ta yi, domin taimakawa wajen kwashe daliban Najeriya da suka makale a Kherson, Ukraine.
Ya tabbatar wa jakadan cewa, gwamnatin Rasha za ta ba da taimakon da ya dace, domin tabbatar da tsaro da jin dadin ‘yan Najeriya a Tarayyar Rasha.
A yayin tattaunawar ta su, an tattauna halin da ake ciki a Ukraine, da kuma batutuwa da dama da suka shafi ci gaban dangantakar abokantaka tsakanin Rasha da Najeriya a nan gaba.