Jami’an Rasha da ke iko da birnin Kherson na Ukraine sun buƙaci mazauna birnin da su fice daga birnin ba tare da bata lokaci ba, inda jami’an suka ce yakin da sojojin ke yi ya yi tsanani a birnin.
A daidai lokacin da dakarun Ukraine ke ƙara matsawa gaba ta gaɓar yamma da kogin Dnipro, akwai dubbai da ke tsallakawa ta ɗaya ɓangaren.
Mutumin da Rasha ta naɗa a matsayin wanda ke jagorantar gudanar da lamura a birnin na Kherson ya ce gwamnatinsa tana da shirin kwasar aƙalla mazauna birnin 10,000 a duk rana domin kare su daga harin ramuwar gayya daga Ukraine.
Kherson ne dai birni na farko da Rasha ta soma ƙwacewa bayan kutsen da ta yi a Ukraine.
Ana kallon idan Ukraine ta sake ƙwace birnin wani babban ci gaba ne a gare ta a wannan yaƙi