Tawagar bincike daga Majalisar Dinkin Duniya, ta gano kwararan shaidun da suka nuna cewa Rasha ta aikata laifukan yaki a Ukraine, ciki har da cin zarafi ta hanyar lalata da kisa da kuma azabtarwa.
Ta ce an tilastawa ‘yan Ukraine komawa Rasha, inda suka bayyana ana lakada musu duka, da azabtar da su da wutar lantarki.
Shugaban tawagar Erik Mose ya ce ”sojojin Rasha sun yi amfani da manyan makamai wajen kai hare-hare ba tare da la’akkari fararen hula ne a yankunan ba.
Ya kara da cewa ”Mun ga abubuwan da suka daga mana hankali kan yawan mutanen da aka kashe ciki har da kananan yara.
Kwamitin ya bada bayanin cewa hatta kananan yara ba su tsira daga cin zarafi ta hanyar lalata ba, su ma sun fuskanci azabtarwa har da kashe wadanda suka nuna tirjiya.