Wata kotu a Rasha ta yanke wa ɗan jaridar Amurka hukuncin ɗaurin shekara 16 a wani gidan yari mai cike da matakan tsaro, saboda laifin leƙen asiri, bayan an saurari ƙarar cikins sirri, wadda jaridar da yake yi wa aiki ta bayyana da ”abin kunya”
A watan Maris ɗin da ya gabata ne jami’an tsaro suka kama ɗan jaridar mai aiki da jaridar Wall Street Journal (WSJ), a lokacin da yake aika rahoto a birnin Yekaterinburg, mai nisan kilomita 1,600 daga gabashin birnin Moscow.
Masu shigar da ƙara sun zarge shi da aiki da hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA, zargin da Mista Gershkovich da jaridar WSJ da Amurkan suka musanta.
Wannan ne dai karon farko da aka yanke wa ɗan jaridar Amurka hukunci a Rasha tun bayan yaƙin cacar baka da aka ƙare fiye da shekara 30 da suka gabata.
Amurka ta zargi Rasha da riƙe shi domin yin musayar fursunoninta da ke tsare a gidajen yarin ƙasashen waje.