Ma’akatar harkokin wajen Rasha ta bayyana cewa, kasar ta saka wa wasu ‘yan majalisar kasar Birtaniya 287 takunkumi, tana tuhumarsu da “tunzura al’umma domin su kyamaci Rasha”.
Wannan matakin na nufin ‘yan majalisa 213 daga jam’iyyar Conservative da 74 daga jam’iyyar Labour ba za su sami izinin shiga Rasha ba.
Ma’aikatar ta kuma ce tana iya daukan “wasu matakan ladabtarwan” – bayan da Birtaniya ta dauki irin wannan matakin a watan Maris.
Cikin jadawalin da Rasha ta fitar, akwai sunayen wasu ‘yan majalisar da ba sa majalisar a halin yanzu.