Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da dasa nakiyoyi a wata madatsar ruwa da ke yankin Kherson a kudancin kasar wadda ke karkashin ikon sojojin Rashar.
Shugaban ya ce idan har aka lalata cibiyar samar da hasken wutar lantarkin ta Kakhhovka, za su shiga cikin bala’i.
Ya ce: “A bayanan da muka samu madatsar ruwan ta Kakhhovka cike take da nakiyoyi da Æ´an ta’addan Rasha suka dasa.”
Ya ƙara da cewa dubban mutane ne da ke kewayen Kogin Dnipro za su kasance cikin hadarin ambaliya.
Mista Zelensky ya fada wa taron shugabannin Turai a Brussels cewa Rasha na son ba da damar a mayar da wuraren makamashi a matsayin fagen daga.


