Babban hafsan sojan Ukraine ya yi gargaɗin cewa, Rasha na yunƙurin abin da ya kira “yanayin Koriya” a kan Ukraine, bayan ta kasa kama babban birnin ƙasar Kyiv tare da hamɓarar da gwamnati mai ci.
Kyrylo Budano ya ce, niyyar Vladimir Putin ita ce kama Gabashi da Kudancin Ukraine bayan sun gaza samun ci gaba a yaƙin da suke yi.
Idan ya samu damar haɗa kan yankunan, Putin zai yi ƙoƙarin shata layi da zai raba su da sauran ƙasar – kusan dai kamar yadda aka yi bayan yaƙin Koriya.