Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta ce, luguden wutar da Rasha ke yi a kan wuraren da farar hula ke zaune, yunƙuri ne na karya gwiwar mazauna Ukraine.
Cikin bayanan sirri da Birtaniya ke bayarwa a kullum, ma’aikatar ta ce, har yanzu jajircewar sojojin Ukraine na bai wa Rasha mamaki wadda daga baya ta fara kai wa garuruwan Kharkiv da Chernihiv da Mariupol hare-hare.
Birtaniya ta kwatanta ayyukan Rasha a Ukraine da waɗanda ta yi a Syria a 2016 da kuma yaƙin Chechnya a 1999, lokacin da Rasha ta ragargaza gine-gine.
Rahoton ya ce, harin da sojojin Ukraine ke kaiwa kan hanyoyin dako ya haddasa wa dakarun Rasha tsayawa cak ba tare da ci gaba da nausawa ba.