fidelitybank

Rasha na salon irin yakin Syria a Ukraine

Date:

Mataimakin magajin garin Mariupol mai tashar jirgin ruwa, wanda dakarun Rasha suka yi wa kawanya ya zargi sojin na Rasha da yin dabaru irin wadanda aka gani a birnin Aleppo na Syria.

Sergei Orlov ya gaya wa BBC cewa, sojojin Rasha na son birnin ya mika wuya domin su jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Ya ce dabarun sun hada da ruwan makamai ta sama ba kakkautawa , da bata gine-gine, wadanda suka hada da makarantu da asibitoci.

Birnin na Mariupol ya shiga kwana na uku ke nan ba wutar lantarki ba ruwa.

A ‘yan mintunan da suka gabata Sakatare janar na NATO, Jens Stoltenberg, ya ce ƙawancen zai karfafa kariyarsa ta kasa da sama da kuma ta ruwa.

Ya ce, wannan shi ne kutsen soji mafi muni a Turai a tsawon gomman shekaru, inda birane ke karkashin mamaya, ake ruwan wuta a kan makarantu, asibitoci da gidajen jama’a.

Sannan ana yin abubuwan da ba su dace ba a kusa da tashar nukiliya a jiya da dare, inda aka kashe farar hula da yawa ko jikkata su.

Fadan da ake gwabzawa kuma ya yadu zuwa wajen wani birnin na kudancin kasar ta Ukraine, Mykolaiv.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp