Kasar Rasha ta sanya shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo.
Kamfanin dillancin labaran kasar, TASS ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar harkokin cikin gida ta Rasha ta nuna cewa Zelenskiy na cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo amma bai bayar da wani karin bayani ba.
Hakan ya faru ne yayin da Rasha ta bude shari’ar laifuka akan Zelenskyy.
Da yake mayar da martani, Ukraine ta yi watsi da rahoton wanda ta bayyana a matsayin shaida na “rashin bege” na Moscow.
Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce shugaban Rasha Vladimir Putin da kansa na fuskantar kame bisa sammacin kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa.
Sanarwar ta ce: “Muna so mu tunatar da ku cewa, ba kamar sanarwar da Rasha ta bayar ba, takardar sammacin da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar na cafke shugaban Rasha Vladimir Putin bisa zarginsa da aikata laifukan yaki gaskiya ne, kuma za a aiwatar da shi a kasashe 123.”
A cewar ma’aikatar, sanarwar ta Rasha ta kasance “shaida ce ta rashin jin daÉ—in na’ura da farfagandar Rasha, wanda ba zai iya tunanin wata hanyar da za ta jawo hankali ba”.
A cikin watan Fabrairun 2022, Rasha ta ba da sammacin kama wasu ‘yan siyasar Ukraine da sauran ‘yan siyasar Turai.
‘Yan sandan Rasha a cikin watan Fabrairu sun sanya Firayim Ministan Estoniya Kaja Kalas, ministan al’adu na Lithuania da ‘yan majalisar dokokin Latvia da ta gabata cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo domin rusa abubuwan tarihi na zamanin Soviet.