Rasha na neman sake zama mamba, a kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, bayan dakatar da ita sakamakon mamayar Ukraine a bara.
BBC ta samu kwafin takardar da kasar ta aika wa mambobin Majalisar Dinkin Duniya, inda a ciki take gabatar da wasu matakai da ta kira na magance matsalolin take hakkin dan adam a duniya.
Wannan dai na faruwa ne duk da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a ranar litinin ya bayyana laifukan yaki da Rasha ke aikatawa kan fararen hula a Ukraine, kamar azabtarwa da fyade.
Jami’an diflomasiyya sun yi iÆ™irarin cewa Rashar na bai wa Æ™asashe makamai da hatsi don samun kuri’unsu. Za ta fafata da Albaniya da Bulgaria wajen neman kujara a kwamitin a zaben da za a yi a watan gobe