Shugaban Amurka Donald Trump ya ce alamun da ya ke gani sun tabbatar masa cewa Rasha a shirye ta ke ta ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine.
Yayin da yake jawabi a zauren Majalisar Dokokin Amurka – karon farko tun bayan da ya koma kan karagar mulki makonni shida da suka gabata Mista Trump ya ce ta samu wata muhimmiyar wasiƙa daga shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky.
A Cikin wasiƙar Shugaba Zelensky ya ce Ukraine a shirye take domin hawa teburin tattaunawa don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Mista Zelensky ya aike da wasikar ne bayan da Amurka ta dakatar da duk wani tallafin kayan aikin soji zuwa Ukraine.