fidelitybank

Rasha na cigaba da lugudan wuta a Ukraine

Date:

Dakarun Rasha na ci gaba da ruwan wuta a biranen da ke gabashi da kudancin Ukraine, yayin da sojojin na amfani har da makamai masu linzami wajen kai hare-haren.

A birni na biyu mafi girma a Ukraine wato Kharkiv, an shafe tsawon dare ana ɓarin wuta.

Sannan an kai hari da makaman atilare a wasu yankunan Luhansk da Donetsk—inda ake hasashe lamura za su sake muni nan da makwanni – yayin da Rasha ke ƙara girke sojoji a waɗannan yankuna.

Kazalika, an zafafa hare-hare a Mariupol, wanda suka yi wa ƙawanya da luguden wuta fiye da wata ɗaya.

An ƙiyasta kusan mutum 130,000 ne suka maƙale a yankunan.

“Ana yi mana ruwan wuta ta ko’ina, a waje muke girki, ruwan sha ya yi wuya, muna matukar bukatar agaji,” a cewar wata mazauniyar Mariupol.

A wani yankin kuma, Rasha ta lalata wani defon man fetur da ke kusa da birnin Dnipro, sannan sun far wa yankin Vinnytsia da ke tsakiyar Ukraine da kuma Redekhiv da ke yammaci.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp