Shugaban Ukraine ya yi gargadin cewa samun rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen Turai zai iya bai wa Rasha dama, wadda dama tuni take iko da kaso biyar na kasarsa.
Volodymyr Zelensky, ya yi kiran da a ƙara azama wajen aikawa da kasarsa makamai.
Bayanan nasa sun zo ne bayan an samu rashin fahimta tsakanin kasashen turai dake yammaci da gabashi har da wasu daga tsakiyar Turai a kan batun yadda za a taimakawa Ukraine.
A can kuma, Rasha na ta kokari wajen fadada mamaye manyan birane a yankin Doneysk da kuma kara nausawa cikin yankin Luhansk.
A yammacin yankin Lviv, Rashan na ta kai hare haren makamai masu linzami a tashar jirgin kasa inda ta nan ne ake shigarwa da Ukraine duk wani taimakon soji.