Amurka ta yi kira da a saka zafafan takunkmai ga Koriya Ta Arewa bayan gwajin da ta yi a baya-bayan nan na wani makami mai linzami.
Wakiliyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas Greenfield ce ta bayyana haka inda ta zargi Pyongyang da tsokanar faɗa.
Sai dai China da Rasha sun ce, ba za su lamunci saka wasu ƙarin takunkumai ga Koriya Ta Arewa ba.
A ranar Alhamis ne shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ya ziyarci wurin gwajin makamin domin sa ido a yayin gwajin.
Makamin dai yana da nisan zango kuma za a iya harba shi daga wata nahiya zuwa wata kuma rabon da ƙasar ta yi gwajin irinsa tun a 2017.