Barcelona ta sayi dan wasan gaban Brazil Raphinha daga Leeds United kan kudi fan miliyan 55.
An bayyana dan wasan dan kasar Brazil mai shekaru 25 ga magoya bayansa a filin atisayen kungiyar na Catalonia ranar Juma’a.
Raphinha, wanda ya koma Leeds daga kungiyar Rennes ta Faransa kan kudi fam miliyan 17 a shekarar 2020, ya buga wasanni 65 na gasar Premier a kulob din Yorkshire, inda ya ci kwallaye 17, ya kuma taimaka aka zura kwallaye 12.
Leeds United ta jinjinawa Raphinha a wata sanarwa da kungiyar ta fitar da ke tabbatar da tafiyarsa: “Za mu so mu mika godiya ta gaske ga Raphinha saboda kokarin da ya bayar a lokacin yana kungiyar kwallon kafa.
Raphinha ya ci wa Leeds fenariti a wasan da suka yi nasara da ci 2-1 a Brentford a ranar karshe ta kakar 2021/22 da ta tabbatar da matsayin ta a gasar Premier.