A wata hira da aka yi da shi don tunawa da ranar zuciya ta duniya ta 2022 da ake yi kowace ranar 28 ga watan Satumba, Nwankwo Kanu, ya koka da cewa mutane da yawa suna mutuwa a kullum a Najeriya saboda rashin isassun wuraren kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa burinsa shi ne gina wani katafaren asibitin kwararru na zuciya a Najeriya domin taimakawa yara marasa galihu da ke fama da cututtukan zuciya.
Shahararren dan wasan kwallon kafa ya ce idan har aka cimma wannan cibiya za ta cike gibin hamma a bangaren kiwon lafiya domin magance cututtukan da ke da alaka da zuciya da kuma rage yawan yawon bude ido na likitanci zuwa kasashen waje kamar Indiya da Amurka da Afirka ta Kudu da kuma Burtaniya.
Ya kara da cewa “Muna bukatar tallafi daga gwamnatoci, kungiyoyin kamfanoni, ‘yan Najeriya masu kishin kasa don cimma hakan.”
Ya ce kungiyar sa mai zaman kanta ta dauki nauyin yin tiyatar zuciya sama da 600 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2022, inda kashi 80 cikin 100 na ayyukan da aka yi a Indiya.
Fitaccen dan wasan kwallon kafa ya ce sama da yara 200 ne ke cikin jerin masu jiran jinya.
Mista Nwankwo ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika zuwa duba lafiyarsu akai-akai don gano lokacin da suke da matsalolin da suka shafi zuciya don samun kulawar gaggawa.
An yi wa tsohon kyaftin din na Super Eagles tiyata a zuciya a shekarar 1996, domin gyara matsalar bututun da ke damun shi, wanda hakan ya sa ya kafa wata gidauniya da za ta yi maganin cututtukan zuciya da ba a gano ba, da kuma yin tiyata ga kananan yara da matasa na Afirka marasa galihu.