fidelitybank

Ranar Talata za mu tsunduma yajin aiki – Ƙungiyar Ƙwadago

Date:

Kungiyoyin kwadago ta ba da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba a fadin kasa.

Kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka kira da yammacin ranar Talata a babban birnin kasar, Abuja.

Sun bukaci rassansu na jihohi su harhado kan ‘yan kwadago da sauran jama’a don gudanar da jerin zanga-zanga da maci a fadin Najeriya.

Kafofin labarai a Najeriya na cewa sun fahimci cewa shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu sun warware bambance-bambancen da suka sanya kungiyar NLC shiga wani yajin aikin gargadi tsawon kwana biyu, ba tare da takwararsu ta TUC ba.

NLC ta kaurace wa aiki a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Satumba da muke ciki don matsa lamba ga gwamnatin kasar a kan ta shawo kan wahalhalun da ‘yan Najeriya, musamman ma’aikata ke ciki, sakamakon cire tallafin man fetur.

A cewar sanarwar da sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja ya fitar, kungiyoyin na gudanar da taron ne ta intanet.

A lokaci guda kuma, ministan kwadago, Mista Simon Lalong ya roki shugabannin NLC su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati na nan a kan kudurin magance damuwar da suka bijiro da ita.

Ministan – kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito – ya kuma nunar da cewa daya daga cikin manyan bukatun NLC a taron da suka yi na baya, tuni an cimma ta, inda ta ba da umarnin sakin shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota a kasar.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp