Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya matan Najeriya murnar zagayowar ranar mata ta duniya, wanda aka gudanar a fadin duniya a ranar 8 ga watan Maris.
Shugaban ya ce, an yi bikin ne a karkashin taken #Break the Bias, “A Yau don Gobe Mai Dorewa” dama ce, ta yin tunani a kan muhimman ayyukan da mata suke takawa a cikin al’umma, gidaje, mulki, sana’o’i, da kowane fanni na rayuwa.
Buhari ya lura cewa, har yanzu mata ba su kai inda ya kamata su kasance a fagage daban-daban ba, amma ya yi imanin cewa, ba za a iya hana su dadewa ba, saboda a kullum suna tabbatar da cewa, za su iya rike nasu ta kowane bangare, da kuma kowane fanni.
Ya yaba da irin gudunmawar da mata suke bayarwa a wannan gwamnati a matsayin ministoci, masu ba da shawara na musamman, manyan mataimaka na musamman, manyan daraktoci, manyan sakatarorin gwamnati, da sauran su, inda ya yi nuni da cewa suna ja da baya, kuma ba zai yiwu kowa ya raina ma’anarsa ba.
Shugaban ya yi murna da mata da iyaye mata, wadanda zaman lafiyar gida da al’umma ya rataya a wuyansu, yana mai addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, annashuwa, da gamsuwa, yayin da suke bukukuwan yau da kullum.