Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya matasan ƙasar nan murnar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musu.
Cikin wani saƙo da ya wallafa shafinsa na Tuwita, shugaba Tinubu ya ce ”A yayin da kuke bikin ranar Matasa ta Duniya, ku sani cewa ilahirin ƙasarmu na tare da ku, domin taimaka muku cimma burinku”.
Tinubu ya kuma yi kira ga matasan da su yi ƙoƙari wajen fuskantar ƙalubalen da ke gabansu, domin cimma burikansu.
”Ku ci gaba da zama jakadun ƙasarmu na gari, kasancewar makomar ƙasarmu na hannunku”, in ji Tinubu