fidelitybank

Ranar 24 jami’ar ABU za ta koma makaranta

Date:

Biyo bayan dakatar da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi na tsawon watanni takwas, jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), ta sanar da ranar 24 ga Oktoba, 2022 a matsayin ranar da za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ilimi.

Majalisar Dattawa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ce ta cimma matsayar.

Daraktan hulda da jama’a na Jami’ar, Auwalu Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce an cimma matsayar ne a taron gaggawar da ta gudanar 516 biyo bayan dakatar da yajin aikin da ASUU ta yi.

Sanarwar ta ce, a zamanta na farko a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, a zamanta 513, majalisar ta amince da ranar, inda ta kara da cewa saboda yajin aikin ASUU da aka tsawaita, a yanzu majalisar ta sauya ranar zuwa 24 ga watan Oktoba 2022.

Ya ce jami’ar za ta koma ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, 2022, inda ta kara da cewa an shawarci dalibai da su lura da sabuwar ranar, saboda za a fara gudanar da harkokin karatu na yau da kullun.

Haka kuma ta yi kira ga daliban da su rike sabuwar kalandar jami’a ta yadda za ta yi musu jagora domin ba za a samu uzuri ga duk dalibin da ya yi biris da ranar da za a ci gaba da karatu ba.

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...
X whatsapp