Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta sanar da shirinta na fara rajistar masu zaɓe a Najeriya, wadda hukumar ta ce za a fara daga ranar 18 ga watan Agustan wannan shekara ta 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a jiya Juma’a.
Ta ce za a buɗe rajistar ne a shafin hukumar a ranar 18, sannan mutane za su fara zuwa cibiyoyin rajistar da hukumar ta tanada daga ranar 25 ga watan na Agusta.
Ta ƙara da cewa za a riƙa zuwa rajistar ne a ofisoshin ƙnananan hukumomin da sauran cibiyoyin hukumar ke faɗin ƙasar.