Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Mauricio Pochettino, ya ce Sergio Ramos zai iya taka leda a gasar Coupe de France da kungiyar Feignies-Aulnoye na mataki na biyar a ranar Lahadi.
Ramos dai ya buga wa PSG wasa sau daya kacal tun bayan da ya zo daga Real Madrid a kyauta saboda raunin da ya ji.
Tsohon mai tsaron baya ya buga wasansa na farko da a ka dade a na jira a wasan da su ka yi da Saint-Etienne a watan da ya gabata, amma matsalolin ciwon tsoka sun ƙare rike shi.