Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na shirin halartar taron zaman lafiya a birnin Alkhariya ranar Asabar, domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen rikicin Isra’ila da Gaza.
Shugaban ƙasar Masar ya gayyace shi ne don shiga tattaunawar, wadda za ta shafi “rikicin Isra’ila da Zirin Gaza, da buƙatar taimakon gaggawa da kuma yin kira a dawo da shirin zaman lafiya”, in ji fadar shugaban Afirka ta Kudu a cikin wata sanarwa.
Ya ce Ramaphosa ya damu matuƙa game da hare-haren da ake kai wa fararen hula, da matsugunan mutane da kuma buƙatar jin ƙai a Zirin Gaza.
A baya shugaban na Afirka ta Kudu ya ce a shirye yake ya shiga tsakani a rikicin Isra’ila da Falasɗinu.
Ya ce al’ummarsa za su iya yin amfani da ƙwarewar da suke da ita na magance rikice-rikice a Afirka da ma sauran su.


