fidelitybank

Rakumin Daawa ya kashe wata Jaririya a Afrika Kudu

Date:

Wata jaririya ta rasu bayan da wani rakumin dawa ya tattake ta a wani gandun namun daji a Afirka ta kudu yayin da mahaifiyar jaririyar ke asibiti cikin mawuyacin hali.

Jaririyar ‘yar wata 16 tana tare ne da mahaifiyarta a wani daga cikin gidaje na alfarma da ke gandun daji na Kuleni Game Park a lardin KwaZulu-Natal.

‘Yan-sanda sun gaya wa BBC cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, amma dai sun fara gudanar da bincike.

Ba abu ne da aka saba gani ba rakumin dawa wanda kusan ga shi nan da yawa a gidajen namun daji da gandun daji a Afirka ta Kudu, ya far ma mutane.

Jami’in ‘yan-sanda Laftana Nqobile Madlala ya gaya wa BBC cewa faruwar abin ke da wuya aka garzaya da uwar da jaririyarta zuwa dakin likita da ke kusa inda a can jaririyar ta rasu.

Ba a dai san takamaimai inda abin ya faru ba a jiya Laraba, a babban gandun wanda yake da masaukin baki na alfarma har guda 14.

Rakumin dawa shi ne dabba mai shayar da nono mafi tsawo a duniya, kuma ba dabba ce da aka sani da fada ba.

Sai dai tamata wadda ita ma idan wani abu ya nemi taba ‘yarta.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp