Dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a zaben Kenya Raila Odinga, ya ce, zai daukaka kara zuwa Kotun Kolin kasar don kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa William Ruto nasara.
Mr Ruto ya samu nasara a kan abokin takararsa Raila Odinga da kasshi 50.5 cikin 100 na kuri’un da aka kada. In ji BBC.
Da misalin karfe 11 na safe agogon GMT, Mr Odinya zai shigar da karar a kotun.
Kazalika ya bukaci duk wanda ya ga sakamakon zaben shugaban kasar bai yi masa dadi ba da ya shigar da kara.
Mr Odinga zai shigar da karar ne bisa la’akari da cewa hudu daga cikin kwamishinonin zabe bakwai sun yi watsi da sakamakon zaben.
A shekarar 2017 kotun koli Kenya sai da soke zaben shugaban kasar saboda rashin sahihancinsa, sannan ta bayar da umarnin a sake sabo a cikin kwana 60.


