Kamfanin dilancin labaran Reuters ya ce, ya samu shaidu da ke tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun rinka ɓarar da juna-biyu ga mata na tsawon shekara 9, musaman mata da Boko Haram ke yi wa ciki.
Galibin waɗannan matan Boko Haram ne suka yi garkuwa da su da kuma yi musu Fyaɗe a yankunan arewa maso gabashin Najeriya.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta wannan zargi.
Rahoto na Reuters na cewa shirin na ɓarar da cikin mata – akalla mata dubu 10 aka ɓararwa ciki ba tare da amincewarsu ba.
Reuters ya tattauna da mata 33 da ‘yan mata da suka shaida yada aka tilasta cire musu cikin da suke ɗauke da shi, a lokacin da suke riƙe a hannun sojoji.
Matan sun ce ana yi musu allurai da ɗura musu magunguna ɓarar da ciki.
Kafar labaran ta kuma tattauna da wasu jami’an kiwon lafiya biyar da na tsaro 9 da ake gudanar da wannan aikin da su.
An dai ɓarar da galibin wannan ciki ne a cikin watan Nuwamban bara.
Sai dai kamfanin labaran bai iya tantace ko tabbatar da sojojin ko gwamnatin da ta kirkiri wannan shiri na ɓarar da cikin matan ba.
A makon da ya gabata, kafin fitar da wannan rahoton, ma’aikatar tsaro ta ƙasa ta yi fatali da binciken Reuters ta na mai cewa babu gaskiya a ciki, kuma cin mutunci ne ga al’ummar Najeriya da al’adunsu.