Rundunar ‘yansanda ta karyata wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan’Adam ta Amnesty International ta fitar da ke cewa an kashe mutum 13 a yayin zanga-zangar da ake yi a kasar, wadda aka fara ranar Alhamis 1 ga watan Agustan nan.
Haka kuma rundunar a musanta ikirarin da kungiyar ta yi na cewa da gangan jami’an tsaro suna amfani da dabaru don kashe mutane, a yayin da suke kula da taruka tare kuma da amfani da bindigogi wajen tarwatsa zanga-zanga.
Dangane da alkaluman mutanen da suka mutu, wanda rundunar ta karyata na kungiyar ta ce gabadaya mutanen da aka rasa a lokacin zanga-zangar bakwai ne, wasu ba ma a sanadin zanga-zangar ba ma suka mutu.
A sanarwar da kakakin ‘yansandan na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce, a tsawon kwana biyu na zanga-zangar, mutum hudu sun mutu, talatin da hudu kuma suka samu raunuka a jihar Borno a wani hari na ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.
Sannan ya ce wasu mutum biyu kuma a masu zanga-zanga sun mutu bayan da wani mai mota kirar Honda ya kutsa cikinsu, kuma yanzu haka ana neman direban wanda ya tsere ya bar motar.
Ya kara da cewa can a karamar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi kuma wani dan kungiyar sa-kai ta bijilanti ya harbi wani daga cikin masu zanga-zanga da suke satar kayan mutane, inda mutumin ya mutu.
Kakakin ya ce bayan wadannan da ya bayyana mutum bakwai babu wani da ya mutu a lokacin zanga-zangar.
Sai dai an samu yadda wasu ke fashi da makami da barnatawa da satar kayan jama’a da na hukuma da sauransu a lokacin a cewar kakakin.
Rundunar ta kuma karya cewa jami’anta na amfani da bindiga, inda kakakin ya ce jami’ansu na aiki cikin tsanaki da kwarewa kamar yadda ya kamata, suna amfani da hayaki mai sa hawaye ne kawai domin tarwatsa jama’a idan abu ya yi kamari.
Rundunar ta kuma ce mutanen da ta kama ta tsare a lokacin zanga-zangar, ba wai kama su ta yi ba, kawai ta rike su ne tana gudanar da bincike.
A don haka ta yi gargadi kan bayar da bayanan da ba na gaskiya ba a kan zanga-zangar.