Rahotanni daga Umuahia, babban birnin jihar Abia, na nuni da cewa an mayar da wurin da za a gudanar da fadar sakamakon zaben gwamnan jihar Abia zuwa Abuja, daga Umuahia.
Yanzu haka jamiāan INEC a Abuja ne za su bayyana wanda ya lashe zaben ranar Asabar, kamar yadda wata majiya daga Umuahia ta bayyana.
Matakin bayyana sakamakon a Abuja, shine don kaucewa tashin hankalin hedkwatar INEC Umuahia wanda ya jinkirta bayyana sakamakon zaben gwamna, kwanaki 3 da kammala zaben.
Karanta Wannan:Ā Zan aiwatar da gwamnati mai tsarin demokradiya a Kaduna – Uba Sani
Daga cikin wadanda ake kyautata zaton sun koma Abuja sun hada da Farfesa Nnenna Oti, jamiāin kula da masu kada kuriāa, Clement Oha, sakataren gwamnati da sauran jamiāan da suka dawo.
Manyan jamiāan jamāiyyar PDP da na Labour Party daga Abia su ma sun je Abuja domin fafatawa na karshe.
A ranar Litinin din da ta gabata ne INEC ta mayar da tattara sakamakon Obingwa zuwa ranar Talata bayan takaddamar da ta barke a jihar sakamakon zarge-zargen zabe da kuma mamaye ofishin Obingwa da wasu āyan bangar siyasa suka yi.
Hukumar ta sanar a ranar Litinin cewa tawagarta daga Abuja za ta isa Abia ranar Talata domin duba sakamakon karamar hukumar Obingwa da sauran wasu yankunan jihar.
Amma a kokarin yin aiki daga wuri mai aminci da dacewa, alkalan zaben sun koma babban birnin kasar.
Da aka tuntubi jamiāin hulda da jamaāa na INEC a Abia, Mista Bamidele Oyetunji, ya tabbatar da cewa manyan jamiāan INEC na jihar Abia sun yi tattaki zuwa Abuja domin ganawa da su.
Bamidele ya ki tabbatar da ko za a sanar da sakamakon zaben gwamna a Abuja ko aāa.
Magoya bayan jam’iyyar Labour 1,000 da suka mamaye mahadar INEC a birnin, sun bukaci a ayyana dan takarar jam’iyyar, Alex Otti a matsayin wanda ya lashe zaben.
Haka kuma, an ga wasu magoya bayan Okey Ahaiwe na PDP suna rera cewa PDP ta doke jamāiyyar Labour a zaben.
Jamiāan āyan sanda a mahadar INEC/CBN sun sha dagule a lokacin da suke sarrafa jamaāar da ke tururuwa.
āDon Allah babu bukatar yin zanga-zanga a nan saboda sun kai sakamakon Abujaā, an ji wani dan sanda yana ba magoya bayan jamāiyyar Labour da suka yi zanga-zanga shawara.