fidelitybank

Rabon tallafi ba na iya ‘yan APC ba ne na kawo ne – Buni

Date:

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce, rabon kayan abinci da ake yi a jihar ba na ‘yan jam’iyyar APC kadai ba ne, na dukkan ‘yan jihar ne.

Buni ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da rabon kayan abinci iri-iri ga matsugunai 3,000 a Damagum, hedikwatar karamar hukumar Fune ta jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa, domin tabbatar da daidaito da adalci, kwamitin jihar ya kunshi shugaban jam’iyyun adawa, Nigerian Labour Congress, (NLC), Trade Union Congress, (TUC), Nigeria Union of Teachers, (NUT).

Sauran sun hada da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, (NULGE), kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), kungiyoyin farar hula da kuma wakilan nakasassu da dai sauransu.

Ya kara da cewa dalilin raba kayan tallafin shine don rage wahalhalun da ake samu sakamakon cire tallafin man fetur.

“Cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ba wai don ya cutar da Najeriya ba ne, sai dai don sanya kasar nan a matsayi mai kyau na ci gaban tattalin arziki mai dorewa”, in ji shi.

Gwamna Buni ya kuma yi gargadin cewa an bullo da hanyoyin da kwamitin rabon kayayyakin da aka raba domin tantance wadanda za su sayar da kayayyakin da aka raba

An tattaro cewa mutane 400,000 a fadin kananan hukumomi 17 na jihar ne ake shirin yin hakan.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp