‘Yan gudun hira daga birnin Mariupol na Ukraine na gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Kyiv domin nuna adawa da kuri’ar raba-gardama da ake yi a wasu yankunan kasar.
Oleh Sukhov, mai shekara 34, ya ce duk da cewa a yanzu yana zaune ne a birnin Kyiv, yana daukar kansa a matsayin dan birnin Mariupol
Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a yanzu ba shi da damar da zai kada kuri’ar, amma ya ce yana so birnin ya ci gaba da kasancewa a kasar Ukraine.
Wata matar mai suna Yana Koshova, mai shekara 33, ta ce tana jin takaicin abinda ke faruwa a birnin wanda ya kasance mahaifa a gareta. In jiBBC.
”Birnin baya bukatar kuri’ar raba-gardama. Mu ‘yan Ukraine ne kuma muna son ci gaba da zama a kasarmu, da garuruwanmu” in ji Yana Koshova.