Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ƙaddamar da asibitin kulawa da marasa lafiya kyauta, musamman mata masu juna biyu da ƙananan yara a babban birnin jihar.
Asibitin wanda wata gidauniyar taimaka wa al’umma ta Maiwada Global ta gina, an samar da shi ne a cikin birnin na Katsina.
Wanda ya gina asibitin, Haruna Maiwada ya ce an samar da asibitin ne “Domin tallafa wa a’ummar yankin da magani da kulawa kyauta”.
Gwamnan jihar, Dikko Radda ya bayyana cewa, gina asibitin zai taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na inganta lafiyar al’umma da rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta wajen samun magunguna da kulawar ƙwarrarun likitoci.
Katsina na daga cikin jihohin da ƙananan yara ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki wanda ke haifar da tamowa.
Ƙungiyar likitoci masu bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa (MSF), a cikin wani rahoto da ta fitar cikin wannan wata na Disamba, ta ce matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ƙananan yara a wasu yankunan jihar ta Katsina “ya nunka idan aka kwatanta da bara”.