Ofishin jakadancin Qatar a Najeriya ya tabbatar da cewa za a yi taron kasuwanci da zuba jari tsakanin ƴan kasuwar ƙasar da na Najeriya a ranar Lahadi mai zuwa.
Tabbacin ya biyo bayan wata wasiƙa da ta ɓulla, wadda ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta aikewa Najeriya, ta ce ganawar ba za ta yiwu ba, domin babu wata yarjejeniya ta bunƙasa zuba hannun jari tsakanin ƙasashen biyu.
Sai dai mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin watsa labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ce ɓata gari ne suka yaɗa takardar, kuma bayanta an tabbatar da cewa za a yi ganawar.
Inda ya ƙara da cewa ƴan kasuwan Najeriya ne suka buƙaci a yi taron don yin amfani da damar ziyarar da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu zai kai ta kwanaki biyu a Qatar.
A yayin ziyarar ta ranar Asabar da Lahadi mai zuwa, ana sa ran Shugaban Najeriya zai yi tattaunawa ta kololuwa da hukumomin Qatar kan yarjejeniyoyi da batutuwan tattalin arziki.