Tsohon kocin Super Eagles, Sunday Oliseh ya tabbatar da cewa, zai yi aiki a karkashin tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger, a lokacin gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.
FIFA ta zabi Oliseh a matsayin daya daga cikin kwararru shida da za su halarci gasar.
Tsohon dan wasan Borussia Dortmund ya saka hotonsa da Wenger da wasu mutane hudu a shafin Twitter a safiyar ranar Asabar.
Ya yi taken: “HaÉ—u da Æ™wararrun fasaha na 6 a Qatar, wanda FIFA Worldwide ta tattara don kawo muku Ingantattun Intelligence Football (EFI’S) na kowane wasa a Æ™arÆ™ashin jagorancin “Sir” Arsene Wenger; Klinnsman, Zaccheroni, Cha, Oliseh, Mondragon da Zubi.
“Kuna iya samun kwasfan fayiloli kai tsaye bayan kowane wasa daga FIFA.”
Oliseh ba zai sake duba duk wani wasa da ya shafi Najeriya ba, yayin da Super Eagles ta sha kashi a hannun Ghana a gasar neman cancantar shiga gasar.