Yau za a fara wasannin gasar cin kofin duniya na kwallon kafa a kasar Qatar.
Wannan ne karo na 22 da za a gudanar da gasar kuma irinta ta farko a wata ƙasar Larabawa.
Kazalika, wannan ne kuma karon farko da za a gudanar da gasar ba a watan Yuni ko Yuli ba.
Tuni Qatar ta tanadi filayen wasa takwas da za a buga wasannin, kuma za a bude wasan farko ne a filin wasa na Al Bayt, Qatar mai masaukin baki za ta kara da Ecuador.
Karo na hudu ke nan da kasashen biyu za su buga wasa a tsakaninsu.
Tawagogin ƙasashe 32 ne za su kece raini a gasar: 13 daga nahiyar Turai, shida daga Asiya, huɗu daga Kudancin Amurka, huɗu daga arewaci da tsakiyar Amurka, da yankin Caribbean mai tawaga hudu, sai kuma nahiyar Afirka mai biyar.
Kasar Faransa ce mai rike da kofin, wanda ta lashe a Rasha a 2018.
A ranar 18 ga watan Disambar 2022 za a kammala gasar.